Daga Maryam Muhammad

Cibiyar Samar da zaman lafiya da sasantawa (IPCR) ta nuna damuwarta akan kalubalen da tsaro ke fuskanta a fadin duniya.

Cibiyar tayi nuni da cewar kyama da tsangwama ya jefa wasu daga cikin mutane bunkasa ta’addanci.

Babban daractan cibiyar Dr Bakut Bakut Wanda ya shugabanci sashin bincike Na cibiyar Dakta Joseph Ochogwu ya wakilta ya Sanar da hakane yayin bude taron hadin kai da zaman lafiya na biyar da suka yi a Babban birnin tarayya Abuja da hadin kan gidauniyar tattaunawa UFUK.

ya tabbatar da cewa soyayya da iya zama da mutane nada muhimmanci wurin kawar da matsalolin tsaro,wanda a yanzu ana amfani da kafofin sadarwa Na zamani domin kalaman matanci da kuma hura wutar ta’addanci.

A karshe yace ana sa ran cewar wata rana za’a kawar da matsalar tsaron muddin kowa zai dauki akidar so da kuma kauna wurin zama da mabanbanta addini ko akida a tsakaninsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: