Ma aikatar lafiya a Najeriya ta tabbatar da ɓullar cutar numfashi ta corona virus a ƙasar.

Cikin sanarwar da ma aikatar ta fitar a shafinta na twitter ta ce wani ɗan ƙasar italiya ne ya shigo ɗauke da cutar bayan ya sauka a birnin legas.

Tuni aka ƙara tsaurara matakai don kare kamuwa da cutar a Najeriya.

Shi kuwa yana can asibiti bayan da gwaji ya tabbatar cewa yana ɗauke da cutar.

Cutar numfashi ta corona virus na ƙara yaɗuwa a ƙasashen duniya da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: