Connect with us

Labarai

Mataimakiyar shugaban ƙasar Iran ta kamu da cutar Corona Virus

Published

on

Daga Jamil Yakasai

Daya daga cikin mataimakiyar shugaban kasar Iran takamo da cutar Corona virus

Ebtekar – daya daga cikin mataimakan shugaban kasar Iran ta kamu da corona virus
Mataimakiyar shugaban kasar Iran na daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar da suka kamu da cutar corona virus a baya-bayan nan.

Gwamnatin Iran ta sanar da mutuwar mutum 26 ta dalilin coronavirus da ta kama mutum 245 a kasar.

Manyan jami’an gwamnatin kasar sun kamu da cutar, ciki har da mataimakiyar shugaban kasar da mataimakin Ministan Lafiya Iraj Harirchi.

‘Yan majalisar dokokin kasar guda biyu na daga cikin wadanda da suka kamu da cutar. Daya daga cikin ‘yan majalisar ya fito ne daga birnin Qom.

”Yaduwar cutar coronavirus a Iran na iya fin yadda ake zato,” in ji Michael Ryan na Hukumar Lafiya ta Duniya.

Ya ce duk da cewa kasar na da ”ingantaccen bangaren lafiya,” mutuwar kashi 10% na masu cutar a kasar na nufin gwajin da ake yi ba ya gano masu cutar idan ba ta yi tsanani ba.

Ma’aikatar Lafiyar Iran ta bukaci ‘yan kasar da su guji yin tafiye-tafiye a kasar sai in yin hakan ya zama dole.

Makwabtan kasar sun rufe iyakokinsu da ita, yayin da aka samu bullar cutar a Hadaddiyar Daular Larabawa, da Kuwaita da Bahrain da Lebanon da Afghanistan da Pakistan, da Estonia, yawancinsu bayan dawowarsu daga Iran.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Bayan Ya Rasa Tikitin Takarar Gwamnan Kaduna Shehu Sani Ya Ce Babu Bambamci Tsakanin Deleget Ɗin PDP Da Ƴan Bindiga Da Ke Karɓar Kuɗi

Published

on

Tsohon Sanata kuma ɗan takarar gwamna, Shehu Sani, ya soki sakamakon zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Kaduna.

Sani ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa ne ya karkata akalar zaɓen inda wakilai ke karɓar kuɗi domin kaɗa ƙuri’ar waɗanda ba su cancanta ba.

Ya ce, “Babu bambanci tsakanin ƴan fashi da ke karɓar kuɗin fansa da wakilai masu karɓar kuɗi don kaɗa ƙuri’a.”

Sani dai ya sha alwashin ba zai ba wa wakilai cin hanci domin su zaɓe shi ba.

“Babu wanda ya isa ya biya kowane wakili a madadina. Ban yi imani da al’adun siyasa na biyan kuɗi don zaɓe ba.

A gabanin zaɓen ranar Laraba, Sani ya ce
Hakan bai dace da aƙida na ba.

Sani wanda ya samu ƙuri’u biyu kacal ya sha kaye a hannun tsohon ɗan majalisar wakilai Isah Ashiru a takarar neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PDP.

Continue Reading

Labarai

Kotu Ta Yankewa Wani Rago Daurin Shekara Uku Agidan Yari

Published

on

An yanke wa wani rago hukuncin daurin shekaru uku a gidan gyaran hali bayan an rahoto cewa ya tunkuri wata mata hakan kuma ya yi sanadin mutuwarta.

Ragon ya kai wa Adhieu Chaping, mai shekaru 45 hari, ya tunkure ta a kirji sau da dama kafin daga bisani ta rasu a karshen makon da ya gabata.

A cikin hukuncin da aka yanke masa, ragon zai shafe shekaru uku a daure a wani barikin sojoji bayan masu sarautun gargajiya a Sudan sun yanke masa hukunci kamar yadda News Week ta rahoto.

Wannan hukuncin na zuwa ne bayan mai ragon ya amince zai biya iyalan mamaciyar diyya da shanu guda biyar.

Hukumomi sun tabbatar da cewa iyalan mamaciyar sun yarda a basu shanu biyar bayan masu sarautan gargagiya sun shiga tsakani.

A cewar wani jami’i a unguwar mai suna Paul Adhong Majak, masu ragon yan uwan mamaciyar ne kuma makwabta ne.

An rahoto cewa za a mika ragon ga iyalan Chaping bayan ya kammala zaman gidan yarin.

Iyalan biyu sun ratabba hannu kan yarjejeniyar amincewa da hakan da yan sanda da mutanen gari a matsayin shaidu.

Continue Reading

Labarai

Saura Ƙiris A Yiwa Abba Ƙyari Kisan Gilla A Gidan Yarin Da Ake Tsare Da Shi

Published

on

Jami’an gidan yari na tunanin mayar da ɗan sandan da aka dakatar Abba Kyari zuwa gidan yarin Kuje bayan da wasu fursunoni suka kusa kashe shi, waɗanda suka zarge shi da rashin gaskiya a cinikin cin hanci a lokacin da yake gidan yari.

Cikin wasu bayanai da muka samu sun bayyana cewa, an kai harin ne a ranar 4 ga watan Mayu, watanni baya wanda Abba Kyari, ke fuskantar shari’ar da ake yi masa na laifukan da suka shafi muggan kwayoyi, aka tsare shi.

Maharan nasa sun kai kimanin 190, in ji wani jami’i, kuma galibinsu suna gidan yari saboda laifukan muggan kwayoyi.

Abba Kyari, mai shekaru 47, mataimakin kwamishinan ƴan sanda, wani ɗan sanda ne da aka yi wa ado, kuma shugaban jiga-jigan jami’an Leƙen asiri na Sufeto-Janar na ƴan sanda kafin faɗuwar sa.

Da farko, an dakatar da shi daga aikin ƴan sanda bayan da masu binciken Amurka suka bayyana sunansa a watan Yulin da ya gabata a matsayin wanda ke da hannu a cikin shirin zamba da kuɗaɗen ƙasa da ƙasa na Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Daga nan kuma, yayin da aka dakatar da shi kuma jiran sakamakon binciken cikin gida, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) a watan Fabrairu ta zarge shi da hannu a wata makarkashiyar safarar miyagun kwayoyi.

Hukumar ta fitar da wani faifan bidiyo wanda Abba Kyari ya bayyana yana bayyana yadda ya yi amfani da tawagarsa wajen tura miyagun kwayoyi da kuma tattaunawa a kan raba wata dukiya mai laifi.

An gurfanar da shi a gaban kotu a watan Maris kuma aka tsare shi a kurkukun Kuje.

“Dodgy yace ɗan sanda na karɓar cin hanci
Maharan na Kuje sun yi ikirarin cewa Abba Kyari ya gurfanar da su a gaban kuliya duk da karɓar cin hanci daga hannunsu, inji majiyar mu.

Ɗaya daga cikin majiyoyin, wani jami’in bincike na jihar kuma jami’in leken asiri, ya bayyana Abba Kyari a matsayin “mai laifi.”

Ba a taɓa samun Abba Kyari da wani laifi ba kuma ya ce ba shi da laifi daga zargin da ake tuhumarsa da shi.

Da yake zantawa da fursunonin, majiyar mu ta ce Abba Kyari yana “kawar da kananan dillalai (magunguna) don share fage ga Afam Ukatu,” wani da ake zargin hamshakin attajirin nan mai sayar da magunguna da ake zargin yana da hannu wajen cinikin Tramadol naira biliyan 3 da ake alaƙantawa da Mista Kyari.

Fursunonin sun yi iƙirarin cewa bayan kama su, Abba Kyari ya buƙaci a ba su cin hanci don ya kashe lamarin, sannan ya ci gaba da gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji wata majiya ta gidan yarin Kuje da ta samu shaidar fursunonin.

Kakakin hukumar gyaran fuska ta Najeriya Francis Enobore ya musanta harin da aka kai wa Abba Kyari. Amma wasu rahotanni sun tabbatar da faruwar harin daga jami’an da ke da masaniya kai tsaye da kuma takardun cikin hukumar.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: