Wasu mahara sun kashe aƙalla mutane 51 a ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

A ranar lahadin da ta gabata ne maharan suka shiga da misalin ƙarfe 6 na safe kuma suka hallaka mutane tare da jikkata wasu.
Mutanen da suka rasa ransu tuni aka binnesu da yammacin jiya lahadi yayinda aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka aaibiti don kula da lafiyarsu.

Hare haren ƴan tada ƙayar baya a Kaduna na cigaba da zuwa ne bayan da aka samu kai hare hare a jihohin Zamfara da Katsina.
