Tare da
Jamilu lawan yakasai

An samu wani magani a cibiyar albarkatun kasa ta Nigeriya (BION), dake sa ran zai kawo karshen wannan sabuwar cuta mai kisa wacce ta samo asali a kasar China, mai suna Coronavirus.
Shugaban cibiyar, farfesa Maurice Iwu, shine ya bayyana hakan shekaran jiya Litinin a birnin tarayya Abuja, yayin da jagoranci wata tawagar masu bincike na kimiyya dan ya nuna sabon magannin.

“Ta bakin farfesa Iwu musu bayani Lamar haka munzo nan ne domin naji muku bayani akan magannin da muka samu da muke tunanin zai kawo karshen cutar nan ta Coronavirus”

Shine farfesa Maurice Iwu, wanda yake tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, yasanar da tawagar wacce ke dauke da Ministoci aciki cewar, kwayoyin da suka hada da magannin sun nuna gagarumar nasara wajen rigakafin cutar SARS “wacce take kama wajen lumfashi mutum” wacce manazarta ke nazarin tafi cutar ta Coronavirus hadari.
“Ashekarar 2014 dai aka sami bullar cutar Ebola mutane da yawa sunyi mamakin yadda aka yi muka samo magannin wanda ta samo asali tun shekara 15 da suka wuce”
“Yanzu kuma da wannan sabuwar cutar ta Coronavirus ta samo asali, yana da matukar muhimmanci mu nemo mafita tun kafin lamari ya gagari kundila” a cewar shi
Shi dai wannan farfesa yace sunfara gabatar da binciken magannin ne a jami’ar Nigeriya ta Nsukka, a lokacin dayake farfesa bangaren Pharmacognosy, sai kuma acigaba da bincike akasar Amurka sanda ya ziyarci kasar.
Farfesa Iwu yace wannan magani da suka samo a cibiyar (BION) akwai alamu masu karfi da suke nuni da cewar zai iya magance wannan babbar annoba ta Coronavirus.
Dr Ogbonayya Ono shine Ministan kimiya da fasaha, yace gwamnatin tarayya tana da tabbacin cewar masana a fannin kimiyya ta Nigeriya zasu nemo magannin cutar ta Coronavirus da kuma zazzabin cutar Lassa.