gwamnatin Najeriya na neman bashin ne don rage ratar da sauran kasashe suka ba ta wajen samar da ababen more rayuwa, musammamn ma ruwan sha da sufuri.

Kusan kashi 70 na wannan rance, wato sama da dala biliyan 17, zai fito ne daga bankin kasar China na EXIM Bank, bankin da ya shafe kusan shekaru 20 yana baiwa Najeriya rance.
Baya ga China, sauran wadanda zasu baiwa kasar rance dai sune: bankin duniya, wanda zai bada sama da dala bilyan biyu, sai bankin bunkasa kasashen Afrika wanda zai bada kusan dala biliyan biyu akwai bankin Musulunci da za a karbi sama da dala miliyan dari a gunsa da hukumar hadin kan kasashe ta Japan, wato Japan International Cooperation Agency (JlCA) da za ta bada dala miliyan 200 cif banki bunkasa kasashe na Jamus, wato, German Development Bank (KFW) shi ma zai bada dala miliyan dari sai hukumar bunkasa kasashe na Faransa; wato the French Development Agency (AFD) da zai baiwa Najeriya rancen sama da dala miliyan dari.
Rfi hausa ta rawaito cewa

Baya ga wannan bashi da Najeriya za ta Ciyo, akwai wanda ta karba tun a shekarar 2002 daga China.
Wannan rance da ake daf da ciyowa, da kuma wanda aka ciyo tuntuni, ya sa yanzu Najeriya za ta kwashe shekaru kusan ashirin tana biyan kudin ruwa.
