Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama ƴan daba 205 da wuƙaƙe sababbi fil guda 636 sai wasu mutane da ake zargi da aikata fashi da makami da garkuwa da mutane.

A yayin da yake jawabi yayin da aka yi holen masu laifuka a helkwatar rundunar da ke Bompai, Kwamishinan ƴan sandan Kano Habu Ahmadu Sani (Kallamu Waheed) ta bakin kakakin ƴan sanda DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an samu muggan makamai masu tarin yawa daga hannun ƴan fashi da masu garkuwa da mutane.
Cikin makaman da aka kama akwai bindiga ƙirar AK47 ƙirar gida da ta waje, da sauran bindigu da harsashi.


Haka zalika an samu nasarar kwato wuƙaƙe sababbi fil, tare da kamo ƴan daba masu tarin yawa.
Sannan ƴan sandan sun kama ganyen tabar wiwi da sholisho har ma da allurar maye masu yawa.
Cikin mutanen da aka kama akwai masu damfara da masu satar motoci harma da waɗanda ke sojan gona tare da mallakar katin shaidar aikin ɗan sanda da kuma kayan soji.
Kwamishinan ya bayyana waɗannnan nasararori cewar sun samu ne ta hanyar haɗin kan da al umma suke bayarwa, haka zalika ya yi kira ga jama da su kadance masu cigaba da bawa jami an tsaro haɗin kai don wanzar da zaman lafiya a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
A wani cigaban kuma an ƙaddamar da littafin da ya ƙunshi illoli da shaye shaye kan haifar a tsakanin matasa.
Kwamishinan ƴan sandan Kano Habu A. Sani ne ya ƙaddamar da littafin a harabar rundunar da ke unguwar Bompai.
Ambasada Mukhtar Gashash ne ya yi wannan yunƙurin jagorantar ƙaddamar da littafin wanda ya ce za a rabawa dɗalibai a jihar Kano da ma sauran jihohin Najeriya.
An fara bawa wasu daga cikin shugabannin ɗalibai a jihar Kano , kuma littafin ya ƙunshi illolin shaye shaye da hanyoyin kare kai daga faɗawa ɗabi ar shaye shaye.