Daga Jamilu Yakasai

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Usman Nagogo, ya tabbatar da kama wasu kansilolin jihar Zamfara bisa zarginsu da hannu a sace wasu kansiloli 4 a karamar hukumar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da sace kansilolin a makon jiya. Kansilolin da aka sace sune kamar haka;

Murtala Arzika na mazabar Gayari,

Lawal AC Milan na mazabar Ubandoma da Sahabi Abubakar na mazabar Birnin Tudu

An sace su ne a hanyarsu ta zuwa Gusau daga Gummi.

Da yake gabatar da masu laifi a hedikwatar rundunar ‘yan sadan jihar Zamfara da ke Gusau, kwamishina Nagogo ya bayyana cewa har yanzu rundunar ‘yan sanda na gudanar da bincike a kan batun sace kansilolin.

“Da farko ban so yin magana a kan yin garkuwa da kansilolin ba saboda har yanzu muna gudanar da bincike a kan maganar.

“Mun gano cewa akwai siyasa a cikin lamarin, musamman idan aka yi la’akari da yadda aka sace su.

“Akwai fasinja guda daya da ya sauka daga motar a hanya bayan an umarci dukkan na cikin motar a kan kar su sanar da kowa, hatta iyalansu, a kan inda zasu je,” a cewar Nagogo.

Da yake amsa tambaya a kan rahoton cewa daya daga cikin kansiloli ya samu kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane, sai Nagogo ya bayyana cewa hakan na daga cikin abubuwan da suke bincike saboda kansilan ya gudu, har yanzu kuma basu san inda yake ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: