Daga Jamilu Lawan yakasai

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke kasar Italiya ta tabbatar da cewar dan wasanta, Daniele Rugani, ya kamu da cutar Coronavirus.

A daren jiya Laraba ne kungiyar ta wallafa a shafinta na twitter cewa, Rugani, ya kamu da cutar, duk da har izuwa yanzu bai fara nuna alamun kamuwa da cutar ba,
gwajin da aka yi masa ya nuna cewa dan wasan na baya ya kamu da cutar da ke ta ruruwa a kasar ta Italiya kamar wutar daji.

Rugani mai shekaru 25, bai doka wasan da kungiyarsa ta samu nasara akan Inter Milan da ci 2 da nema ba, a ranar 8 ga watan Maris.

Zuwa yanzu dai an killace Rugani don gudun kar ya yada cutar ga makusantansa da kuma ragowar ‘yan wasan na Juventus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: