Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

A karon farko Ganduje ya halarci sallar juma’a tare da sabon sarkin Kano

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da sallar juma a masallacin kwaryar birnin kano tare da sabon sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Gwamnan ya halarci sallar tare da rakiyar mataimakinsa dakta Nasiru Yusif Gawuna da sauran muƙarrabai a gwamnatinsa.

Babban limamin jihar Kano Farfesa Muhammad Sani Zahraddin ne ya jagoranci sallar bayan ya gabatar da huɗuba kamar yadda aka saba.

Bayan idar da sallar ne kuma gwamna Ganduje ya ziyarci katafariyar gadar sama da ake ginawa a ƙofar mata.

Cikin sanarwar da babban sakataren watsa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar ya ce, gwamnan ya ja hankalin masu kasuwanci a wuraren da su kula sosai kasancewar ana aiki da manyan injina masu ƙarfi a wajen.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: