Daga Bashir Muhammad

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bawa yan wasanta Umarni kowa ya killace kansa sabo da fargabar kamuwa da cutar corona Virus.

Kungiyar ta dauki wannan matakin ne bayan samun dan wasan kungiyar mai buga kwallon kwando dauke da cutar.

Haka zalika kungiyar tace ya zama
wajibi ta dauki irin wannan matakin ganin yadda yan wasan kwallon kafar kungiyar dana kwallon kwando suna amfani da bandaki dayane.

Dama tun a farkon makon nan hukumar shirya gasar Lalila ta kasar Sifaniya ta haramtawa yan kallo shiga kallon wasa ,wanda a yanzu ta dage wasan wannan makon sakamakon samun dan wasan Real dauke da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: