Wani babban jami’i a kasar China ya bayyana cewa sojojin kasar Amurka ne suka kai musu cutar Corona virus a kasar , duk kuwa da bai bayar da wata kwakkwarar shaida ba.

Mai magana da yawun ma’aikatar kasashen waje na kasar china Zhao Lijian, shine ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a karshen makon da ya gabata.

Idan ba a manta ba a baya shugaban cibiyar kula da manyan cutuka da bakin shi ya bayyana cewa cutar ta samo asali ne ta hanyar sayar da namun daji da ake yi a kasuwannin birnin na Wuhan.

Amma ‘sai gashi wani babban jami’i a kasar ta China, kuma masani a fannin lafiya ya zargi cewa cutar ta samo asali ne daga wani waje daban,

A cikin rubutun da ya wallafa, Zhao ya sanya bidiyo na cibiyar lura da manyan cutuka ta kasar Amurka, inda ya tabbatar da cewa wasu ‘yan Amurka da suka mutu sanadiyyar mura, an tabbatar da samun cutar a jikinsu.

Sakataren kasar Amurka mike Pompoe ya fusata bayan jin kalaman Yan kasar ta China, da suka bayyana Cutar ta samo asali ne daga kasarmAmurka.

A yanzu dai sama da mutane Dari da talatin 130,000 ne suka kamu da cutar, sannan kusan mutum dubu biyar 5,000 ne suka mutu a fadin duniya sanadiyyar cutar.

Robert O’Brien, mai bada shawara ta musamman a fannin tsaro na kasar Amurka, bayyana cewa cutar ta samo asali ne daga kasar China.
A wani cigaban kuma
Ma’aikatar lafiyar Italiya tace annobar coronavirus ta halaka ‘yan kasar 368 cikin kwana 1, abinda ke tabbatar da kasar a matsayin sabuwar cibiyar annobar cutar bayan China.
Yanzu haka dai adadin mutanen da cutar murar ta halaka a kasar ta Italiya ya kai dubu 1 da 809, sama da rabin yawan mutanen da annobar ta kashe a wajen kasar China.

Leave a Reply

%d bloggers like this: