Dan majalisa Mai Wakiltar Warawa a majalisar Dokokin jihar kano Hon Labaran Madari ya kalubalanci Shugaban majalisar Dokokin jihar AbdulAziz Garba Gafasa.

Bisa Matakin da ya dauka na Dakatar dasu na Tsawon Watanni shida daga majalisar.

Acewar Madari wannan Mataki ya sabawa Dokokin jihar kano, kuma sun yi da na sanin Zaben Shi matsayin Shugaban majalisar.

Hon Labaran Madari ya bayyana hakan ne A lokacin da yake ganawa da manema labarai a jiya kamar yadda majiyar mu ta Solace Base ta rawaito.

Majalisar dai ta dauki Matakin Dakatar da Yan majalisun guda biyar ne biyo bayan ta da hargitsi da sukayi a majalisar tare da hana zaman majalisar a ranar.

Yan majalisun da aka Dakatar sun hada: da Hon. Garba Ya’u Gwarmai dan majalisa mai wakiltar mazabun Kunchi/Tsanyawa, da Hon. Labaran Abdul Madari dan majalisa mai wakiltar mazabar Warawa, sai Hon. Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar Gezawa , da Hon. Mohammed Bello Butu Butu dan majalisa mai wakiltar mazabun Rimingado/Tofa sai kuma Hon. Salisu Ahmed Gwangwazo dan majalisa mai wakiltar mazabar birnin Kano.

Yan majlisun sun tada hargitsi ne a lokacin da Kwamitin da aka bawa bincikar Korafin da aka Kai Kan tsohon sarkin Kano Muhammad sunusi ll.

Leave a Reply

%d bloggers like this: