Shugaban hukumar tace fina finai a Kano ya garzaya kotu musulunci da ke Hausawa a Kano don neman haƙƙinsa a kan wani zargi da akai a kansa..

Kotun shari ar musulunci da ke hausawa a Kano ta fara sauraron koken da shugaban hukumar tace fina finai a Kano Mallam Isma ila Na Abba Afakallahu na zargin da yake a kan wasu kudaɗe da yayi zargin ya ci.
Kotun ta aike da takardar sammaci ga Baban Chinedu kan wani faifan bidiyo da ya yi na zargin shugaban hukumar da cinye wani kuɗi da aka bayar tallafi ga iyalan marigayi Ibro.

Kotun ta saka ranar 1 ga watan Afrulu mai kamawa don fara sauraron kowanne ɓangare tare da zaƙulo gaskiyar lamari.
