A ƙoƙarinsa don ganin an yiwa tufkar hanci, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ƙaddamar da kwamitin kar ta kwana daƙile afkuwar cutar numfashi ta Corona Virus.

Gwamnan ya samar da kayan aiki tare da samar da wuri na musamman don killace mutanen da ke ɗauke da ita ko da an samu a Kano.

Manyan likitoci daga jami ar Bayero ne ke cikin kwamitin wanda mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Gawuna  ke jagoranta.

Har yanzu dai ba a samu ɓullar cutat a Kano ba amna an yi hakan da nufin kandagarki don gudun ko da ta kwana.

Wuraren da zai zamo cikin kulawar kwamitin ciki har da filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: