Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Gwamnatin Kano ta haramta tarukan biki a jihar

Gwamnan jihar Kano ya tabbatar da hakan yayin da yake yiwa al ummar Kano jawabi kan ɓullar annubar cutar numfashi ta Corona Virus.

Gqamna Abdullahi Umar Ganduje umarci ma aikatar kula da al adu don rufe dukkanin wurin wasanni da tarukan da gidan adana kayan tarihi a jihar.

Cikin jawabin da yayi na kimanin mintuna ƙasa da 30 gwamnan ya ce gamnatin jihar na yin duk mai yuwuwa don ganin an tsame al umma daga kamuwa da cutar Corona Virus.

Cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka akwai samar da kwamitin kar ta kwana na musamman wanda zai yi aiki a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Gwamnan ya roƙi maau riƙe da sarautar gargajiya da malaman addini da su taƙaita al ummar da ke halartar wuraren ibada don gudun yaɗuwar cutar.

Sannan ya shawarci al umma da su kasance maau tsafta tare da bin dukkan hanyoyin da masana suka bada shawara don kaucewa kamuwa da cutar ciki har da taƙaita cakuɗuwar al umma da suka zarta 20.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: