Gwamnatin jihar Kano ta sake samar da wurin da za a killace masu ɗauke da cutar sarƙewar numfashi ta corona virus a jihar.

Gwamnatin ta ƙara samar da wurin killace masu ɗauke da cutar ne a kwanar dawaki a Kano.

Duk da cewa har zuwa yanzu ba a samu ɓullar cutar a jihar ba, gwamnatin na ɗaukar matakin ne don daƙile afkuwa ko yaɗuwar cutar a cikin al umma.

Tun tuni gwamnatin ta samar da kwamitin kar ta kwana a kan lamarin wanda mataimakin gwamnann ke jagoranta.

Cikin matakan da gwamnatin ke ɗauka akwai samar da wuraren killace jamar da ke ɗauke da uta wanda ke ɗake da kayan aiki a cikinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: