Cikin wata da sanarwar da fadar shugaban kasar Najeriya ta fitar ta ce shugaba Buhari ya amince da bai wa gwamnatin Jihar lagos naira biliyan 10 a matsayin tallafi domin yaki da cutar a matsayin ta na jihar da tafi samun masu dauke da ita.

Shugaban kasa ya amince da bukatar kwaso kwararrun likitocin Najeriya da ke Congo Brazzaville wajen samun horo a wajen Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya domin ba da gudumawa a gida.

Muhammad Buhari ya kuma bada umarnin kara yawan kayan gwaji da na aikin likitoci da kuma yawan wuraren gwajin da kuma kiran jami’an kiwon lafiya da suka yi ritaya domin bada gudunmawar su.

Gwamnatin Najeriya ta kuma sanar da rufe iyakokin kasar na makwanni 4 da hana jiragen sama daga kasashen duniya tashi da sauka a kasar da kuma mayar da sansanin tashin alhazai a matsayin inda za a killace wadanda suka kamu da cutar a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: