Connect with us

Labaran jiha

Gwamnan kano yayi Kira da Al’ummar jihar kano da Su dau Azumi Gobe Litinin, Don neman tsari daga Annobar Covid 19

Published

on

Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje yayi Kira ga Al’ummar jihar kano da Su dau Azumi a Gobe Litinin 30 ga watan Maris,Don yin Addu’a wajen kiyaye Bullar Cutar Corona Virus a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kafa Kwamitin da zasu Samar da kudin tallafin da za’a dakile Cutar Corona Virus a jihar.

Ganduje ya kafa Kwamitin ne karkashin Jagorancin Farfesa Muhammmad yahuza Bello, shugaban jam’iyar Bayero Ta kano.

Ragowar Yan Kwamitin sun hada da

Alhaji Tajudeen Aminu Dantata, Mataimakin shugaba,

Sanata Barau Jibrin, mamba,

Rt. Hon. Abdulaziz Garba Gafasa, Speaker Kano State

House of Assembly – mamba

Alhaji Yusuf Nabahani, Madakin Kano – Mamba

Alhaji Salisu Sambajo,wakilin. Alhaji Aliko Dangote – Mamba

Alhaji Karami Isyaka Rabi’u, wakilin Alhaji Abdussamad
Isyaka Rabi’u memba

Alhaji Dalhatu Abubakar Al-Amsad, President

KACCIMA – Memba

Alhaji Mudassir Idi Abubakar – Memba

Alhaji Abdullahi Abbas, Kano APC Chairman – Memba

Alhaji Nasiru Aliko Koki – Memba

IPAC Chairman, Kano – Memba

Murtala Sule Garo, Kwamishinan kananan hukumomi Memba

Mal. Muhammad Garba, Kwamishinan yada labarai – Memba

Dr. Zahra’u Umar Muhammad,

Kwamishiniyar Al’amuran mata da walwalarsu – Memba

Dr. Muhammad Tahar Adamu, Kwamishinan harkokin addinai – Memba

Hon. Lamin Sani, Kano ALGON Chairman – Memba

Prof. Abdu Salihi, Kano Integrity Group – Memba

Alhaji Haruna Zago – Memba

Ustaz Yusuf Makwarari – Memba

Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan – Memba

Sheikh Haroun Ibn Sina – Memba

CAN President, Kano – Memba

Eze Ndi Igdo, Kano – Memba

Oba of Yoruba, Kano – Memba

Hajiya Aishatu Ja’afar, S.A. Social Intervention – Memba

Wakilin Ofishin NEMA,na kano – Memba

Comr. Abbas Ibrahim, shugaban Kungiyar Yan jaridu Reshen jihar kano – Memba

Barrister Abdul Adamu Fagge, NBA Kano – Memba

Comr. Ibrahim Adamu, Umbrella of Kano Concerned

Civil Society Groups – Memba

Red Cross, Kano – Membea

SP Abdulkadir Haruna Hadejia, Kano Police

Command – Memba

Yusuf Dawaki – Memba

Nigeria Civil Defence Corp,

Kano State – Memba

Kano State Vigilante Group – Memba

Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, Permanent Secretary,

REPA – Secretary

Click to comment

Leave a Reply

Labaran jiha

Sarkin Musulmi Ya Nada Gwamna Nasir Na Kebbi A Matsayin Gwarzon Daular Usmaniyya

Published

on

Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na lll ya nada gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris a sarautar gwarzon daular Usmaniyya.

 

Wakilin Sarkin Musulmi kuma sarkin Argungun Alhaji Samaila Muhammed Mera ne ya mika takardar nadin ga gwamnan a gidan gwamnatin Jihar ta Kebbi a jiya Juma’a.

 

Alhaji Sa’ad ya nada gwamna Nasir ne a sarautar ta Gwarzon Daular Usmaniyya ne bisa gudummuwar da yake bayarwa na taimakon al’ummar kasar.

 

Sarkin Muslumin ya bayyana cewa sarautar gwarzon daular Usmaniyya ana bayar da ita ne ga dukkan wanda ya sadaukar da kansa wajen taimakon al’ummar Jiharsa da dama Kasarsa baki daya.

 

Sarkin na Argungu ya kara da cewa masarautar Sarkin Musulmi na sa ne da irin gudummawa taimako da kuma kyautatawar da gwamnan ya ke bayarwa a wajen inganta rayuwar al’umma.

 

Acewar Argungun Majalisar masarautar sarkin Musulmi za ta bayyana ranar da za ta nadawa gwamnan rawanin sarautar nan ba da dadewa ba.

 

A yayin karbar takardar nadin gwamna Nasir ya mika godiyarsa ga masarautar sarkin Musulmi bisa dacewar da ta gani ta nadashi a matsayin.

 

Sannan gwamna Nasir ya ce gwamnatinsa da mutanen Jihar za su samar da lokaci domin zuwa yin godiya fadar Sarkin Musulmin da ke Jihar Sokoto domin nuna farin cikinsu da nadin da aka yi masa.

Continue Reading

Labaran jiha

Gwamnan Legas Ya Yiwa Fursunoni Afuwa

Published

on

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayar da umarni sakin fursunoni 55 daga gidajen gyaran hali daban-daban na fadin jihar.

Kwamishinam shari’a na jihar, Lawal Pedro, SAN, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu.

Gwamna ya amince da sakin mazauna gidan gyaran halin ne bisa shawarwarin da majalisar duba yiwuwar yiwa fursunoni afuwa ta jihar.

Continue Reading

Labaran jiha

Babu Batun Rikici Tsakanin Kwankwaso Da Abba – Gwamnatin Kano

Published

on

Wasu rahotannin na nuni da cewa, bayan ci gaba da fuskantar rikice-riciken cikin gida da ake ci gaba da fuskanta a jam’iyyar NNPP a Kano, gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya daina daga Wayar uban gidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin abubuwa da suka kara rura wutar rikicin jam’iyyar ciki harda batun nada Kwamishinoni.

Hakan ya sanya gwamna Abba Kabir ya gujewa haduwa da jagoran nasa Rabi u Kwankwaso.

Sai dai bayan bullar takun sakar da ya fara shiga tsakanin Kwankwaso da Abba, gwamnatin Jihar ta Kano ta fito ta musantan jita-jitar da ke yawo cewa baraka ta kunno kai tsakanin gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf da ubangidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, har ta kai ga baya daga wayarsa.

Hadimin gwamnan na musamman kan shafukan sada zumunta Salisu Yahya Hotoro ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na facebook a yau Litinin.

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa ko kadan babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa akan Kwakwaso da Abba.

Acewar Hotoro har yanzu akwai alaka mai karfi tsakanin Kwankwaso da Abba, babu wani abu da ta shiga tsakaninsu.

Gwamnatin ta Kano ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ba ta da tushe balle makama.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: