Shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya Muhammmad Babandede ya bayyana cewa yana dauke da Cutar Corona Virus.

Babandede ya bayyana hakan ne kafar sada zumunta na WatsaP inda ya aike wa manema labarai.

Babandede ya ce ya na dauke da Cutar ne tun bayan da ya dawo daga kasar Burtaniya tun a ranar 22 ga watan Maris, tare da Killace kansa.

Shugaban yayi Kira da daukacin Al’ummar Najeriya da Ma’aikatan hukumar shige da fice da su sanya shi cikin addu’a.

Ya Kuma you Kira da Ma’aikatan hukumar dasu cigana da aiki tare da Mataimakin sa kamar yadda suka saba

Leave a Reply

%d bloggers like this: