wasu mahara dauke da makamai sun yi awon gaba da wasu Yan Kasar Chana a jihar Ebonyi a jiya.

Lamarin dai ya faru ne a garin Ishiagu Dake karamar hukumar IVO na jihar Ebonyi.
Shaidun gani da ido dai sun bayyana cewa maharan sun sace Yan chanan ne su Uku daga bisani suka sako daya daga cikin su.

Kwamishinan yansandan jihar Awosola Awotunde ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an sace Yan chanan ne Dake aikin hako ma’adanai na kamfanin Green Field.

A cewarsa Wayanda aka sace sun hada da Shen Gusmeh da Mao Xinmin.
Ya kuma tabbatar da cewa Rundunar yansandan tana kokari don ganin ta ceto su cikin koshin lafiya.