Daga Maryam Muhammmad

Tun bayan dokar da gwamnatin jihar Kano ta kafa na rufe iyakokin jihar tare da shige da fice don killace yaduwar annobar Covid 19,
hukumar Karota ta gargadi direbobin daukar kaya dake shigowa jihar nan da su gujewa daukar fasinjoji don gujewa fadawa fishin hukumar.

Shugaban hukumar Karota Alh Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakane,cikin wata sanarwa da ya fitar.

Inda jami’in Hulda da jama’a na hukumar Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar.
yace hukumar ta lura cewar wasu daga cikin direbobin daukar kayan suna saba dokar da gwamnatin jihar nan ta kafa, inda suke shigo da fasinjoji Wanda hakan ya sabawa umarnin gwamnatin.
Haka kuma hukumar ta gargadi masu manyan motocin da su tilastawa direbobin su bin umarnin gwamnati har zuwa lokacin da gwamnati zata janye wannan dokar.