Majalisar wakilan kasar Najeriya tace zata yi wani dokar gaggawa da zai bawa hukumar wutan Lantarki ta bada wuta Kyauta na Tsawon Watanni biyu.

Wannann Matakin ya biyo bayan yadda wannan annobar Covid 19 ta sanya Gwamnati sanya mutane su Rika zama a gida.
Shugaban majalisar Femi Gbajabiamila shine ya bayyana hakan inda yace hakan zai taimaka wajen habbaka Tattalin Arzikin kasa Wanda ya samu nakasu.

Wannan doka za’a tattauna akan sa ne bayan majalisar ta dawo daga hutun da ta tafi na dan lokaci.
