A jihar Kano an ƙara tsaurara jami an da ke kula da tabbatar da bin dokar da gwamnati ta saka na hana shige da fice da ma ziga-zirga.
A yau litinin da aka shiga rana ta huɗu bayan da aka saka dokar, an sake tsaurara matakai don ganin an tabbatar da bin doka da oda a jihar.
Cikin jerin zagayen sa ido da Mujallar Matashiya ta fita a yau, an gano jami an tsaro na gudanar da tsauraran binceke kafin mutanen da aka amince su yi zirga zirga a jiharsu wuce.
Sai dai da yawa daga cikin jami an na kokawa ganin cewar ba a tanadar musu komai da za su kula da lafiyar kansu ba.
Sannan babu wani tanadi na abinci ko sha ko wani guziri da aka basu.
Cikin zagayen namu na yau mun leƙa ɗaya daga cikin wuraren da aka tanada don killace maau ɗauke da cutar Corona a Kano, wanda ke filin wasa na Sani Abacha, mun tarar da cewar har yanzu ba a kammala aikin ba sannan akwai jami ai da ke kula da haramar wurin.
Hanyoyin shige da ficen jihohi sun kasance cikin tsauri ganin yadda har yanzu jama a ke kukan cewar wasu daga wasu jihohin na ahigowa garin Kano duk da dokar hana shige da fice da ma zirga zirga a jihar Kano.