Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka a Najeriya NCDC ta tabbatar da cewar an samu mutane 23 da suke ɗauke da cutar a Kano.

Cikin sanarwar da ta wallafa a daren yau, hukumar ta ce jimillar mutanem da cutar ta harba a Najeriya yau sun kai 38.
Jimillar masu ɗauke da cutar mutane 665 ne a Najeriya

Sai wadanda aka sallama mutum 188, sannan waɗanda suka mutu mutum 22.
