Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bai wa jiharsa tallafin kudade domin yaki da coronavirus.

Ganduje ya Bukaci hakan ne a yayin wata ziyara da Darakta Janar na Hukumar Yaki da Yaduwar Cutttuka ta Najeriya, NCDC, Dr. Chikwe Ihekweazu ya kai masa.
Don sanin irin matakan da jihar Kano ta yi wajen tunkarar wannan annoba, da yake Dada ta’azzara a jihar dama duniya baki daya.

Ganduje ya ce, sun samu sama da miliyan 500 da wasu kayayyaki da za a fara raba su nan kusa ga al’umma,

Ya Kuma ce sun kafa kwamitocin da za su tabbatar cewa, talakawa sun samu tallafin rage radadin da coronavirus ta jefa su a ciki.
Sai dai duk da wannan yunkurin da gwamnatin, tayi har zuwa yanzu babu wani tallafi daga gwamnatin tarayya,
duk da cewa, Kano ce ta uku a jerin jihohin da suka fi fama da wannan annoba a Najeriya a cewar gwamnan.