Gwamnatin Tarayya ta shirya fara dawo da yan Najeriya da annobar Coronavirus ta rutsa da su a kasashen waje.

Minista Harkokin Waje Geoffrey Onyeama ne ya bayyana haka a yayin taron kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 a ranar Litinin.
Ministan yace za’a debo ‘yan Najeriyan ne mutum 200 daga kasashe daban daban.

Wanda yanzu haka an samu Jirage biyu da suka amince zasuyi jigilar mutanen a cikin farashi Mai Rahusa.

Fiye da ‘Yan Najeriya 2,000 a kasar Amurka, Birtaniya, Dubai, China da sauran kasashe ne suka yi rajistan dawowa gida Najeriya bayan sun amince da sharuddan da gwamnati ta gindaya musu.
Daga cikin sharuddan zasu biya kudin jigilarsu, kuma za’a gudanar da gwajin cutar Coronavirus a kan su, sa’annan a killace su tsawon kwanaki 14 da zarar sun sauka a Abuja ko Legas.
“Saboda karancin wurin killacesu, shi yasa zamu kwaso mutane 200 a kowanne sawu a Abuja da Legas, idan aka kammala killace su bayan kwanaki 14 sai mu sake kwaso wasu mutane 200.” Inji shi.