Cibiyar gwajin Cutar Corona Virus ta jihar kano ta Dakatar da aikin ta.
Babbban Daraktan dake kula da cibiyar Cuttutuka dake Asibitin Koyarwa na malam Aminu Kano
farfesa Isa Abubakar
Shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau.
A cewarsa tun bayan Bullar Cutar Corona Virus a jihar kano aka samu Karancin kayan gwaje gwaje a cibiyar.
Farfesa Isa Abubakar Wanda shine jami’in hulda da jama’a na Asibitin Malama Aminu kano.
Yace cibiyar ya fuskanci matsala ne tun a jiyan bayan samun mutane 44 da za’a gwada su, kuma gashi kayan aikin zai ishi mutane 40 ne kawai a cibiyar.
Wannnan dalilin ne ya sanya Dakatar da Cibiyan daga aiki har sai an samu kayan gwaje gwaje.