Gwamnan jihar kaduna malam Nasir El Rufa’i ya tabbatar da cewa ya Warke daga Cutar Corona Virus da yake dauke dashi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a shafin sa na twita, inda yace bayan gwajin Sakamakon da akayi masa ya nuna cewa baya dauke da Cutar a tare dashi.
El Rufa’i dai ya kai kimanin Makonni 4 a Killace tun bayan da ya bayyana yana dauke da kwayar Cutar Corona Virus.

Jaridar prime ta rawaito cewa Gwaman ya godewa Al’ummar najeriya dama na jihar Kaduna bisa addu’oi da suka rika masa na fatan samun lafiya.
