DAGA RABIU SANUSI KATSINA

Hukumar kula da kare muhalli wadda aka fi sani da (NESREA) ta kasa reshen jihar katsina ta ziyarci wa su hukumomin da su ka hada da asibitin kwararru na gwamnati da ke katsina, da ma’aikatar da ke kula da asibitocin da ta jihar, sai hukumar tsabtacce muhalli ta jiha tare hukumar kula da likitoci ta jihar katsina

Da ya ke bayyanawa wakilin mu na katsina dalilin ziyarar coodinator hukumar na jihar katsina mr Jibrin Inuwa kwankwaso, ya bayyana cewa sun kawo ziyarar ne a matsayin su na Yan sandan kare muhalli yasa su ka zagaya dan bayyana ma sauran hukumomin kula lafiya da tsabtacce muhalli na jihar katsina dokoki da tsare tsaren da ya kamata abi wajen kulawa da ma su cutar covid-19 da muhallin su.

Jibrin kwankwaso, ya kuma kara bayyana cewa da yawa akan yi ma marassa lafiya magani da wa su sinadarai maimakon a samu sauqi, amma sai kaga an samu ya haifar da wata cutar daban a qarshe, sannan kuma shi kanshi tara datti da ake yawan yi yana kara jawo wa su cututtakan.

Mr Jibrin ya qara da cewa kamar yadda ministan su na kasa ya umurci shugaban su na kasa da cewa ya jaddadama sauran shuwagabanin jihohi da su fita dan wayar ma da sauran hukumomin kula lafiya da yadda yakamata suyi kula da marassa lafiya, muhallin da su ke zaune.

a na shi jawabin sakataren hukumar kula da likitoci na jihar katsina Dr Shamsu Usman Yahayya gachi, ya bayyana jin dadin sa da yadda wannan hukumar ta kawo wannan ziyara ofishin su.

Dr Shamsu ya kuma yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da hukumar NESREA ta jiha dan cimma nasara da yaki da duk wata cuta tare da sanin sinadaran da ya kamata ayi amfani da su wajen yima ma su cututtaka magani da su.

Sakataren ya kuma tabbatar da cewa idan allah ya yarda zai gabatar ma da babban kwamitin kula da cutar mashako wannan quduri na su, kuma yana da tabbacin kwamitin zai aiki da wadannan dokokin na Yan sandan kare muhalli na kasa reshen jihar katsina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: