DAGA RABI’U SUNUSI KATSINA

A cigaba da yunkurin dakile hana yaduwar cutar sarkewar Numfashi.
gwamnatin jihar Katsina ta karbi kimanin almajirai 419 Yan asalin jihar Katsina da iyayen su, su ka kai su makarantun tsangaya a jihar Kano.

Dr Mustapha Inuwa wanda shi ne babban sakataren gwamnati jihar katsina ya samu damar karbar almajiran a maimakon gwamnatin jihar Katsina, a sa’ilin da Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Alh, Sanusi Sa’idu Kiru ya damka almajiran a madadin gwamnatin ta Kano.

Gwamnati jihar ta Kano ta yi a kokarinta na tantance almajiran ne ta hanyar hada bayanan su da sunayen su, da su ka dauki lokaci suna yi.
Yayin da mukarraban gwamnati jihar katsina ta karbi almajiran ne a garin gidan mutum daya a karamar hukumar Kusada wadda ta ke kan iyaka da jihar ta Kano ranar Talata.
Sakataren gwamnati jihar katsina Dr Mustapha Muhammad Inuwa, ya tabbatar da cewa gwamnati jihar ta saukar da yaran a farfajiyar ma su yima kasa hidima na jihar katsina dan kara yi ma su gwaje gwaje kafin damka su ga iyayen su.
Dr Mustapha ya kuma kara da cewa gwamnati jihar katsina ta tanadi motocin da za su dauki almajiran yazuwa kananan hukumomin su na jihar bayan kammala gwajin lafiyar su.