Dan wasan gaba kuma jagoran Yan wasan Kasar Najeriya Super Eagle Ahmad Musa ya musanta rade radin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa yana dauke da Cutar Corona Virus.
Ahmad musa dake taka leda a Kungiyar kwallon kafa Ta AlNassar ta kasar Saudiya ya bayyana cewa batun yana dauke Cutar Corona shi da iyalansa karya ne kawai.
Dan wasan ya musanta zargin ne inda ya wallafa a shafin sa na Twita,
Inda yace suna zaune shi da iyalansa a kasar Saudiya a Killace na Tsawon Kwanaki 14.
Don haka yace ayi watsi da irin wannan kagaggen labarai, yana cikin koshin lafiya tare da iyalansa.
Yana kuma Taya Al’ummar musulmin duniya shiga watan Ramadan