Kungiyar Shugabannin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) sun ayyana shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a matsayin gwarzon da zai jagoranci yaki da annobar cutar covid-19 a yankin ta Afrika.

A ranar Alhamis ne shugabannin ECOWAS su ka gudanar da taro ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo.

Mataimakin shugaban kasa na Musamman akan kafafen yada labarai Femi Adesina, ne ya sanar da nadin da aka yi wa Buhari ta cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twita.

ECOWAS ta gudanar da taron ne domin tattaunawa a kan kokarin dakile yaduwar annobar covid-19 a kasashen da ke zaman mamba a kungiyar.

A cikin wata sanarwa da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa akwai kimanin mutum 5,774 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar covid-19 a yankin Afrika ta yamma. Daga cikin adadin mutanen, mutane kimanin 1,616 sun warke, yayin da mutum 147 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kamuwa da kwayar cutar covid-19.

Leave a Reply

%d bloggers like this: