Hukumar da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce ta ware dala miliyan 150, don tallafawa hukumomin kasashe da yankuna 211 da suke karkashin hukumar.
dan rage radadin durkushewar tattalin arzikin da annobar coronavirus ta janyo musu.

Cikin sanarwar da ta fitar a karshen mako, FIFa ta ce kowace hukumar kwallon kafa a matakin kasa za ta samu kason dala dubu 500, idan suka cika ka’idojin cancantar samun tallafin, dake a matsayin kashin farko.

Shugaban FIFA Gianni Infantino yace tallafin na daga cikin shirin da hukumar ta kaddamar a shekarar 2016, na rabawa hukumomin kasashe manbobinta jimillar dala biliyan 1 da miliyan 746, daga shekarar 2019 zuwa 2022.

Majiyar mu Ta Rfi hausa ta rawaito cewa Tun bayan bullar Cutar Corona Virus a birnin Wuhan na China a watan disambar bara.

Cutar na dada yaduwa zuwa sassan duniya, annobar coronavirus zuwa yanzu ta halaka kusan mutane dubu 200, ta haddasa karyewar tattalin arzikin duniya, fannin wasanni kuma na daga bangarorin da tasirin annobar ya durkusar, a don haka hukumar ta yanke shawarar tallafawa Mambobinta dake Sassa daban daban a Duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: