Gwamnonin Najeriya sun baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara da ya dan sassauta dokar hana zirga zirga da aka sanya a wasu Jihohi domin dakile yaduwar cutar coronavirus wadda ke shirin karewa gobe lahadi
Gwamnonin sun bukaci shugaban da ya hana zirga zirga tsakanin Jiha zuwa wata Jiha, amma kuma ya bada izinin zirga zirga a cikin Jihohin domin baiwa jama’a damar walwala.
A wata wasika da suka rubutawa Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha, Gwamnonin sun bukaci hana mutane gudanar da tarurruka da kuma tilasta amfani da kyallen dake rufe fuska.
Wasikar dake dauke da sanya hannun gwamnan Ekiti Kayode Fayemi yace bayan tattaunawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sun amince su gabatar da bukatun su domin sanyawa cikin ayyukan da kwamitin ko ta kwana na gwamnatin Najeriya ke aiki da shi wajen yaki da cutar coronavirus.
Rfi hausa ta rawaito cewa Gwamnonin sun kuma bukaci shugaba Buhari da ya cire masu safarar abinci da kayan marmari da magunguna da kayan asibiti da man fetur da kuma amfanin gona cikin wadanda aka hana zirga zirga