Shugaban kasar Najeriya Muhammdu Buhari ya gargadi Musulmai game da shiga ayyukan ibadar da ka iya zama silar kamuwa da cutar Corona-virus a kasar.

Wannan Kiran ya zo ne a daidai lokacin da aka fara gudanar da azumin watan Ramadan a jiya Juma’a.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya bukaci Musulman da su kauce wa taruwar jama’a wajen bude-baki da sallar jam’i, Kamar yadda kasashen Musulmai na duniya suka dauki wannan Mataki.

Buhari ya bayyana azumin bana a matsayin mai tattare da kalubale, duba da cewa, ya zo ne a cikin wani yanayi da duniya ke fafutukar yaki da cutar coronanvirus.

Shugaban ya kuma bukaci Musulmin Najeriya da su daure su yi amfani da wannan wata wajen gudanar da Addu’oi don kawo karshen wannan Annoba ta Covid 19.

Leave a Reply

%d bloggers like this: