DAGA RABIU SANUSI KATSINA

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bada umurnin a rufe kananan hukumomin Mani da Jibia tun daga karfe bakwai na safiyar alhamis.
Wannan sanarwar na need cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa, yasa ma hannu,sannan sanarwar ta qara dacewa daukar wannan mataki ya biyo bayan samun mutane dai dai daga wadannan kananan hukumomi dauke da kwayar cutar korona.

Idan dai za mu iya tunawa cewa gwamnati jihar katsina ta dauki alwashin garkame dukkan wata qaramar hukumar da aka samu da wanda ya ke dauke da cutar mashaqo a cikinta

Sannan a bukaci jama’ar wadannan kananan hukumomin da su zama ma su biyayya da dukkan dokokin da gwamnati ta dauka dan kare lafiyar su.
Haka kuma kwamitin kula da wannan alhaki zai duba inda mazauna kananan hukumomin za su sayi magunguna da kayan abinci.
Jami’an tsaro na nan dan tabbatar da biyayya ga dokokin gwamnati jihar katsina kamar yadda sanarwar ta bayyana.