Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana kaɗuwarsa bisa yadda ake rasa manya a Kano.

Rashin da aka yi a yau shi ne rasuwar Farfesa Balarabe Maikaba, babban malami a sashen koyon aikin jarida na jami ar Bayero a Kano.
Kafin rasuwarsa an rasa manyar farfesoshi waɗanda auka rasu kafin shi.

Ganduje ya bayyana cewar rashin da ake yi a Kano ba iyalan mamatan ne suka yi rashi ba, rashi ne na duk al umma baki daya.

Gwamna Ganduje ya miƙa saƙon ta aziyyarsa ga ƴan uwa da abokan arziƙi har ma da hukumar gudanarwa ta jami ar Bayero a Kano.