Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar gano daya daga cikin mutum biyu masu dauke da cutar covid 19 da suka arce a jihar Borno.

Kwamishinan lafiya na jihar Borno Dr.Salisu Kwayabura shine ya tabbatar da hakan a shafin Facebook na gwamnatin jihar.

Dr Salisu Yace an gano mara lafiyar mai suna Abbas Kaka Hussain dan shekaru 24 a duniya yau da safe a birnin Maiduguri.

tawagar ma’aikatar lafiya da jami’an tsaro da masu gudanar da bincike ne suka ganoshi a cikin wani mawuyacin hali a gidansa dake unguwar Gwange.

Ya kara da cewa jami’an lafiyar sunyi duk mai yiwuwa domin bashi kulawa tare da gano mutanen da sukayi mu’amala dashi.

Sai dai kwamishinan yace har zuwa yanzu suna cigaba da neman Hauwa Muhammad yar shekara 42 a duniya wadda ta gudu tana dauke da cutar covid 19.

Leave a Reply

%d bloggers like this: