Shugaban kasa Muhammmad buhari ya kara bada Umarnin Rufe jihar Kano ba shiga ba fice na Tsawon mako biyu.

Shugaban ya bayyana hakan ne a daren yau lokacin da yakeyi wa Al’umma kasa bayani ta kafafen yada labarai game da Cutar Corona Virus.

A Jawabin nasa ya nuna damuwa matuka kan yadda ake samun Mace macen mutane a jihar Kano.

Ya koka kan yadda ake tafiyar da harkar kiwon lafiya a jihar, inda ya dau Alwashin bada gagarumin gudummawa wajen yaki da Cutar Covid 19 a jihar dama kasa baki daya.

Haka zalika ya bayyana cewa Umarnin Rufe jihohin da aka samu Bullar Cutar yana daram.

Leave a Reply

%d bloggers like this: