gwamnatin jihar Kaduna ta saka sabon doka na zaman gida dole na tsawon kwanaki 30, gwamnatin ta bayyana cewa ta samar da kotun tafi da gidanka.
Sannan duk gurin ibadar da aka kama ya karya dokar zaman gidan to zai rasa lasisinsa kuma za’a rusheshi.
Wannnan jawabi na dauke ne cikin sanarwar da mai baiwa gwamnan jihar shawara akan sadarwa, Muyiwa Adekeye ya Fitar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa yanzu dolene Idan mutum zai fita daga gidanshi ya saka takunkumin rufe baki da hanci,
gwamnatin tace zata samarwa da marasa karfi abin rufe hancin amma wanda suke da hali su siya su rika amfani dashi.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki wadannan tsauraran matakaine biyo bayan irin yanda cutar ke kara munana a jihohin dake da makwaftaka da jihar Kaduna.