Shugaban kasa Muhammmad buhari yayi ganawar sirri da Da ministan Lafiya Osaghie Ehaniere da shugaban Hukumar dakile yaduwar Cutttuka ta Chikwe Ihekweze

Rahotanni dai sun bayyana cewa ganawar ya biyo samun rahotanni akan yawan Mace mace da ake fama dashi a jihar kano, da ma yadda Cutar Corona Virus ke dada yaduwa.
Sai dai shugaban Hukumar NCDC yace nan bada jimawa ba za’a dawo cigaba fa gwajin Corona Virus a jihar ta kano.

Tun a makon da ya gabata ne ake ta yawan samun Mace mace a jihar kano.
Sai dai har yanzu ba’a San musabbabin yawan mace macen ba.
