Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta taimakawa Najeriya da na’urorin dake taimakawa marasa lafiya numfashi (Ventilators)domin yaki da annobar COVID-19 dake cigaba da yaduwa a kasar.

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ne ya sanar da wannan shirin bayan tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta waya, inda shugaba Buhari ya yiwa Trump bayani kan halin da ake ciki dangane da annobar coronavirus a Najeriya.

Ministan yace tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta mayar da hankali ne kan wannan annoba dake cigaba da janyo asarar rayuka a duniya.

Majiyar mu ta Rfi hausa ta rawaito cewa Trump ya jaddada muhimmancin dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka inda ya bayyana shirin aikawa Najeriyar wadannan injinan taimakawa marasa lafiya numfashi.

A matsayin gudummawar kasar Amurka ga Najeriya wajen yaki da Corona virus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: