DAGA Fatima AbdulHadi Hotoro

Gwamnatin tarayya ta aiko kayan abinci, a cikin tirela guda 110 zuwa jihar kano dan rabawa talakawa a matsayin tallafin dazata basu domin ragemusu radadin dokar nan zaman gida saboda hana yaduwar cutar covid 19.

Wannan Mataki ya biyi bayan Umarnin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayar a litinin na rufe iyakokin jihar kano tsahon sati 2 domin dakile cigaba da dakile yaduwar cutar corona virus datake cigaba da yaduwa a jihar.

Wannan jawabi na kunshe ne cikin wata sanarwa me dauke da sahannun mai taimakawa ministar kula da ayyuka jin kai da tallafawa al’umma Sadiya umar farouk, salisu na’inna danbatta

Inda yace yanzu haka motocin suna kan hanyar isowa kano domin mika kayayyakin abincin da suka hadar da shinkafa da gero masara ,ga gwamnatin kano, dumin rabawa marasa karfi don rage musu radadin zaman gida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: