jarumin a masan’antar Bollywoodfina Irfan Khan ya rasu a yau laraba

Kafin rasuwar marigayin ya fito a manyan fina-finai kamar Lunchbox da Piku da kuma Hindi Medium.
Irfan ya mutu yana da shekaru 53, ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Mumbai a ranar Laraba bayan ya yi fama da ciwon hanji.

Haka kuma marigayin ya mutu ne bayan
Rasuwar Mahaifiyar sa da kwana hudu ne.

Irfan khan shine na Takwas a jerin maza masu kudi a masan’antar Bollywood.
Irfan khan dai mabiyin Addinin musulunci ne.