Tare da Maryam Muhammmad

Jami’ar Bayero dake Kano ta samar da na’urar da zata taimakawa masu dauke da cutar Covid 19 yin numfashi a saukake wato Ventilator.

Jami’ar karkashin kulawar kwararru a tsangayar fasaha, tace duk wasu gwaje gwaje sun gama domin tabbatar da ingancin na’urar, abinda ya rage kawai gwada na’urar a jikin dabbobi kamar yadda yake a ka’ida.

Mataimakin shugaban Jami’ar Bayero farfesa Yahuza Bello yace, adai dai lokacin da ake kashe fiye da Naira miliyan 7 wajen Siyan na’urar ta Ventilator, Jami’ar ta kashe kasa da Naira dubu 500 gurin kera na’urar.

, Jami’ar na shirin yin hadin gwiwa da kamfanin hada motoci kirar Peogeout domin samar da na’urar da yawa domin amfanin al’umma, musammama a wannan lokaci da ake fama da Annobar Cutar Corona Virus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: