Hukumomin lafiya a Najeriya sun ce gwaji ya tabbatar da cewar, likitoci 10 a Kano dake asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sun kamu da cutar coronavirus.

Shugaban kungiyar likitoci masu koyon kwarewa na kasa reshen asibitin na Malam Aminu Kano Abubakar Nagoma, yace likitocin sun kwashi cutar ne a lokacinda suke kula da wasu marasa lafiya da suka zo asibitin dauke da alamun cewar annobar ta coronavirus ce ta shafe su.

Dakta Nagoma yace daga cikin likitoci goman da suka kamu akwai, wadanda ke karbar karin horo na neman kwarewa.

Majiyar mu ta Rfi hausa ta Rawaito cewa A baya bayan nan dai an samu likitoci da dama a sassan Najeriya da suka kamu da cutar coronavirus,
,
bayan da kungiyar likitocin kasar
ta koka kan rashin karfafa basu kayayyakin samun kariya daga annobar, yayin kula da lafiyar wadanda suka kamu.

Jihohin da suka tabbatar da kamuwar wani adadi na likitocinsu dai a baya bayan nan sun hada da Borno inda likitoci 16 suka kamu, sai Legas itama mai likitoci 16, sai kuma 14 a jihar Katsina.

Kafin aukuwar wannan lamari dai, a karshen watan Afrilu Ministan lafiyar Najeriya Osagie Ehanire, ya bayyana cewar ma’aikatan lafiya 113 dake yaki da wannan annobar coronavirus sun kamu da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: