Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa gwamnatocin kasashe kin hada kai wajen yakar annobar coronavirus da shi ya janyo yaduwar Cutar a duniya

Yayin tsokaci kan halin da duniyar ke ciki, Guterres yace rashin hadin kan ne ya baiwa annobar damar yaduwa cikin sauki, tare da hallaka dubban rayuka.

Binciken kwarraru a fannin kimiyya ya cimma matsayar cewar cutar coronavirus ta samo asali daga dabbobi zuwa ga dan Adam, wadda ta bulla a watan disambar shekarar 2019 a wata kasuwar saida naman dabbobi dake birnin Wuhan a kasar China.

A baya bayan nan hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci hukumomin China da su bata damar hada gwiwa da kasar don karin bincike na musamman kan asalin cutar ta coronavirus da ta addabi duniya.

Corona virus dai ta hallaka kimanin mutane dubu 235 da 500 a fadin duniya kasa da awanni biyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: