Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ba zai iya raba jihar Borno da karatun Allo ba, kuma ba zai kulle makarantun Allo ba.

Sai dai Gwamnan yace gwamnatin Borno za ta hana Almajirai yawo a kan hanya da kuma mayar da almajiran da aka kawo su daga nesa gaban iyayensu.
sannan gwamnati za ta taimakawa Malaman Makarantun Allo gwargwadon iko domin su kula da Almajiran dake gabansu.
A cewar sa dole ne abi matakan gyara tsarin Karatun allow jihar, ba Wai hanasu ba.

