Shugaban kwamitin kar ta kwana da fadar shugaba ƙasa ta kafa kan sha anin yawaitar yaɗuwar cutar corona a Kano Dakta Nasiru Gwarzo ya ce sun gano inda matsalar take tare da hanyar maganceta.

Dakta gwarzo ya bayana haka ne yayin da gwamnan Kano Abdullai Umar Gaduje ya halarci wajen bada horo ga ma ikatan lafiya 300 kan yadda za a yaƙi cutar corona virus a Kano.

Sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fita, ya ce gwamna Ganduje ya halarci wajen ne a jiya.

Dakta Gwarzo ya ce duk da kasancewar an samo mafita, haka ba yana nufin mutum ya kwanta bacci yau gobe ya tashi ya ga komai ya daidaita ba, sai an bi koma a sannu daki daki.

An bawa ma aikatan lafiya 300 kan yadda za su bi waje gudanar a aikinsu.

A yain ziyara ne kuma kwamitin ya jinjinwa gwamnatin jihar Kano bisa yadda take ƙoƙarin samar da kayan kare kai daga kamuwa da cutar Covid 19 ga ma aikatan lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: